إعدادات العرض
Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai
Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai
Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili မြန်မာ Русский Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە தமிழ் ไทย دری Fulfulde Magyar ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली Oromoo Wolof Soomaali Български Українська Azərbaycan ქართული тоҷикӣ Македонски bm Malagasyالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi soyuwar zance a wurin Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya. Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai. Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.فوائد الحديث
Sauƙin shari'a, ta inda ba ya cutarwa da kowaccen waɗannan kalmomin ka fara.
التصنيفات
Zikiri da ba su da wani Qaidi