إعدادات العرض
Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan
Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Português മലയാളം తెలుగు မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Kiswahili தமிழ் دری Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Oromoo Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana godiyar da bawa ya ke yi wa Ubangijinsa a kan falalarSa da ni’imarSa suna cikin al’amuran da ake samun yardar Allah da su, idan ya ci abin ci sai ya ce: Na gode wa Allah. Idan ya sha abin sha sai ya ce: Alhamdulillah.فوائد الحديث
Karamcin Allah Mabuwayi, haƙiƙa shi ne ya ba da arziƙi, kuma yake yarda da a gode masa.
Yardar Allah ana samunta da abu mafi sauƙi, kamar godiya ga Allah bayan ci da sha.
Yana daga cikin ladubban ci da sha: Godiya ga Allah maɗaukaki bayan ci da sha.
التصنيفات
Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha