Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai

Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa; Salloli biyar ababen faralantawa a yini da dare ne, da sallar Juma'a a kowane mako, da azimin watan Ramadan a kowacce shekara, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne na kananan zunubai da sharadin nisantar manyan zunubai. Amma manyan zunubai kamar zina da shan giya ba mai kankaresu sai tuba.

فوائد الحديث

Zunubai daga cikinsu akwai kananu a kwai kuma manya.

Kankare kananun zunubai abin shardantawane da nisantar manyan zunuban.

Manyan zunubai su ne zunuban da haddi yazo a cikinsu, ko narko a lahira ya zo a cikinsu, ko fushi, ko akwai tsawatarwa a cikinsu, ko la'anta ga mai aikatasu, kamar zina da shan giya.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Falalar Ayyuka na qwarai, Falalar Sallah