إعدادات العرض
Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma
Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە සිංහල ไทย دری Fulfulde Magyar ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली Oromoo Wolof Soomaali Български Українська Azərbaycan ქართული тоҷикӣ Македонски bm Malagasy yaoالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - yana ƙin mai tsananin husuma, kuma mai yawaitata daga cikin mutane, wanda ba ya karɓar jawuwa ga gaskiya, kuma yana ƙoƙarin tunkuɗeta da jayayyarsa, ko ya yi husuma da gaskiya, sai dai cewa yana kai matuƙa a cikin husuma, kuma yana fita daga iyakar daidaituwa, yana jayayya ba tare da ilimi ba.فوائد الحديث
Neman haƙƙin wanda aka zalunta da gaskiya ta hanyar kai ƙara, ba ya shiga cikin babin husumomi ababen zargi.
Jayayya da husuma suna daga illolin harshe waɗanda suke sabbaba rabuwa da juya baya a tsakaknin musulmai.
Jayayya abar yabo ce, idan ta kasance a kan gaskiya ne kuma usulubinta mai kyau, kuma tana kasancewa abar zargi idan ta kasance don dawo da gaskiya ne da tabbatar da ɓarna, ko ta kasance ba tare da hujja ba ko dalili.