Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma

Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma

Daga Abu Ayyub Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma . zai kasance kamar wanda ya ‘yanta mutane huɗu daga tsatsan (Annabi) Isma’il.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ma’ana: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa. To, duk wanda ya maimaita wannan zikirin a rana sau goma, to, yana da lada misalin ladan wanda ya gusar da bauta daga bayi huɗu cikin zuriyar [Annabi] Isma’il Ɗan [Annabi] Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma ya keɓance zuriyar [Annabi] Isma’il ne amincin Allah ya tabbata a gare shi domin sun fi waɗanda ba su ba.

فوائد الحديث

Falalar wannan zikirin wanda ya ƙunshi kaɗaita Allah maɗaukaki da bauta da mulki da godiya da cikakken iko.

Ana samun ladan wannan zikirin ne idan aka yi shi a jere ko a rarrabe.

التصنيفات

Falalar Zikiri