Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina

Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ruwaitowa daga Ubangijinsa cewa idan bawa ya aikata zunubi sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai ce: Bawana ya aikata zunubi, kuma ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, Ya suturtashi ya yafe masa, ko yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafarta masa. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Ya yi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana, sai ya aikata abin da ya so muddin dai cewa shi a duk lokacin da ya yi zunubi zai bar zunubin ya yi nadama, ya yi niyyar barin komawa a cikinsa, sai dai zuciyarsa tana rinjayarsa, sai ya afka a cikin zunubi karo na gaba, muddin dai yana aikata haka yana zunubi yana tuba, to, zan gafarta masa; domin cewa tuba yana rushe abin da ke kafinsa.

فوائد الحديث

Yalwar rahamar Allah ga bayinsa, kuma cewa mutum a duk lokacin da ya yi zunubi, kuma a duk lokacin da ya aikata idan ya tuba daga shi ya koma zuwa ga Allah Zai yi karɓi tubansa.

Mai imani ga Allah - Maɗaukakin sarki - yana burin afuwar Ubangijinsa, sai ya yi gaggawa zuwa tuba, ba zai zarce a kan saɓo ba.

Sharuɗɗan ingantacciyar tuba: Cirata daga zunubi, da nadama a kansa, da niyya a kan rashin komawa zuwa zunubin, idan tuban ya kasance daga zaluncin bawa ne a dukiya ko mutunci ko rai, sai ka kara sharaɗi na hudu, shine: Warwara daga mai haƙƙin, ko bashi haƙƙinsa.

Muhimmancin sanin Allah wanda ya ke sanya bawa ya zama masani da al'amuran addininsa, sai ya tuba a duk lokacin da ya yi kuskure, ba zai yanke ƙauna ba ba zai zarce ba.

التصنيفات

Falalar Zikiri