Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi

Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi

Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da gode masa. an share kurakuransa an kuma gafarta su, ko da suna da yawa misalin farar kunfar nan ce da take saman teku lokacin kaɗawar igiya da ambaliya.

فوائد الحديث

Wannan ladan yana samuwa ne ga wanda ya faɗeta a rana a jere ko a rarrabe.

Tasbihi: Tsarkake Allah daga tawaya. Godiya: Siffanta Allah da cika tare da so da kuma girmamawa.

Abin nufi da Hadisin kankare ƙananan zunubai, amma manyan dole sai da an tuba.

التصنيفات

Falalar Zikiri