Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun: 1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. 2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu. 3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.

فوائد الحديث

Mafi girman zunubai shi ne yi wa Allah shirka; domin haka ya sanya shi farkon zunubai, kuma mafi girmansu, faɗinSa - maɗaukakin sarki yana ƙarfafa wannan: {Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirka da shi, Yana gafarta koma bayan hakan ga wanda Ya so}.

Girman haƙƙoƙin mahaifa, don Ya gwama haƙƙinsu da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin laifin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddodi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narkon shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasunsu sun fi wasu muni a haramci, ƙananan zunubai kuma su ne waɗanda ba wadannan ba.

التصنيفات

Munanan Halaye, Zargin Savo