إعدادات العرض
Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira
Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira
Daga Abbas ɗan AbdulMuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah, Allah - Mai girma da ɗaukaka -shi. Ya ce: "Ka roƙi Allah lafiya", sai na zauna wasu kwanuka sannan na zo sai na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah shi. Sai ya ce dani: "Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी മലയാളം Kurdî অসমীয়া Kiswahili አማርኛ Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands සිංහල پښتو ไทย नेपाली Кыргызча Malagasy Svenska Română తెలుగు ქართულიالشرح
Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.فوائد الحديث
Maimaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ita kanta addu'ar ga Abbas lokacin da ya tambaye shi karo na biyu yana nuni akan cewa lafiya ita ce mafi alherin abinda bawa zai roƙi UbangijinSa.
Bayanin falalar lafiya, kuma a cikinta akwai tattarowar alherin duniya da lahira.
Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan neman ƙari na ilimi da alheri.
التصنيفات
Addu’o’I da aka samu daga Annabi