Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini

Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini

Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ba da labarin cewa wanda Allah Ya nufe shi da alheri, to, sai ya azurta shi da fahimta a addininSa tsarki ya tabbata a gare shi. Kuma shi [Annabi] tsira da aminci su tabbata a agare shi Mai rabawa ne, yana raba abin da Allah Ya ba shi na arziki da ilimi da wanin haka, Kuma hakikanin wanda yake bayarwar shi ne Allah, amma duk wanda ba shi ba, to, su sabubba ne, ba sa anfanarwa sai da izinin Allah, Kuma lalle wannan al’ummar ba za ta gushe a kan al’amarin Allah ba, wanda ya saɓa musu ba zai taba cutar da su ba , har ƙiyama ta tashi.

فوائد الحديث

Girma da falalar ilimin addini, da koyon shi da kuma kwaɗaitarwa a kansa.

Tsayuwa a kan gaskiya tabbace yake a cikin wannan al’ummar, idan wata jama'a ta kauce sai wata ta ɗauka.

Fahimtar addini yana daga cikin nufatar Allah maɗaukaki na alheri ga bawansa.

Annabi tsara da amincin Allah su tabbata a gare shi kawai yana bayarwa ne da umarnin Allah da ganin damarSa, shi ba ya mallakar komai.

التصنيفات

Falalar Ilimi, Falalar Ilimi