إعدادات العرض
Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana
Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە සිංහල ไทย دری Кыргызча or Kinyarwanda नेपाली Română Lietuvių Malagasy ಕನ್ನಡ Oromoo Nederlands Soomaali Српски Українська Wolof Moore ქართული Azərbaycan Magyar Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.فوائد الحديث
Kwadaitarwa akan taimamkekeniya da toshe bukatun masu rauni.
Ibada ta kunshi kowane aiki na gari, daga ibada akwai kaikawo ga wacce mijinta ya rasu da kuma miskini.
Dan Hubaira ya ce: Abin nufi cewa Allah - Madaukakin sarki - Zai tattaro masa ladan mai azimi da mai tsayuwar (dare) alokaci daya; saboda shi ya tsaya ga matar da mijinta ya rasu a matsayin mijinta..., ya kuma tsaya ga miskinin da ya gajiya daga tsayuwa akan kansa, sai ya ciyar da wannan ragowar abincinsa, ya kuma yi sadaka da karfinsa, sai amfaninsa ya zama ya yi daidai da azimi da tsayuwar dare da kuma yaki.
التصنيفات
Falalar Ayyukan Gavvai