Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale

Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale.

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Umar Allah Ya yarda da shi yana ba da labarin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana su yin abin da zai kawo wahala ba tare da wata buƙata a kan hakan ba, hakan magana ce ko aiki.

فوائد الحديث

Yana daga cikin ƙaƙalen da aka hana: Yawaita tambaya, ko ɗorawa kai abin da ba shi da iliminsa, ko tsanantawa a abinda Allah Ya sauƙaƙa a cikin sa.

Ya kamata ga Musulmi ya koyawa kansa sauƙi, da rashin tsananta wa kai a magana, ko a aiki, a abin cinsa, ko abin sha, da maganganunsa da sauran ayyukansa.

Musulunci addinin sauƙi ne.

التصنيفات

Munanan Halaye