Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne

Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne

Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyya, kaɗai mutum (ana bashi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan ikhlasi, domin cewa Allah ba Ya karɓar aiki sai abin da aka nufi zatinsa da shi.

Ayyukan da ake neman kusancin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da su idan mukallafi ya aikata su a kan tafarkin al'ada, to, ba shi da wani lada a kansu, har sai ya yi nufin neman kusancin Allah da su.

التصنيفات

Ayyukan Zukata