Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya

Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya

An karbo daga Anas Allah Ya yarda da shi, ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba mu labarin Musulmi ba zai kasance mai cikakken imani ba har sai ya gabatar da son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan son babarsa da babansa da ɗansa da ‘yarsa da mutane bakiɗaya, wannan soyayya kuwa tana hukunta yi masa biyayya da taimaka masa da kuma barin saɓa masa.

فوائد الحديث

Wajibcin son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma gabatar da shi a kan son duk wani da a ka halitta.

Daga cikin alamomin cikar so: Taimakawa Sunnar Ma’aikin Allah, da kuma bayar da rai da dukiya a kan haka.

Son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana hukunta yi masa biyayya a abin da ya yi umarni da kuma gasgata shi a abin da ya ba da labari da kuma nisantar abin da ya hana kuma ya tsawatar, da bin Sa, da kuma barin Bid’a.

Haƙƙin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mafi girma mafi ƙarfi a kan na kowa, domin ya kasance shi ne dalilin shiriyarmu daga ɓata da kuma tseratar da mu daga wuta, da rabauta da aljanna.

التصنيفات

Ayyukan Zukata