Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar

Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haramcin zagin matattu da afkawa a cikin mutuncinsu, kuma wannan yana daga munanan ɗabi'u; domin sun kai zuwa abin da suka gabatar da shi na ayyuka na gari ko na banza, kamar yadda wannan zagin ba ya isa zuwa garesu, to, lallai cewa yana cutar da rayayyu.

فوائد الحديث

Hadisin dalili ne a kan haramcin zagin matattu.

Barin zagin matattu a cikinsa akwai kula da maslahar rayayyu, da kiyaye zaman lafiyar jama'a daga gaba da ƙiyayya.

Hikima a kan hana zaginsu, cewa sun isa zuwa abin da suka gabatar, to, zaginsu ba ya amfanarwa, kuma a cikinsa akwai cutarwa ga makusantansa rayayyu.

Cewa ba ya kamata ga mutum ya faɗi abin da babu maslaha a cikinsa.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Falaloli da Ladabai, Mutuwa da Hukunce Hukuncenta, Mutuwa da Hukunce Hukuncenta