Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama

Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi hani game da ƙauracewar musulmi ga ɗan uwansa musulmi sama da dare uku, kowane ɗaya daga cikinsu zai haɗu da ɗayan, amma ba zai yi masa sallama ba, kuma ba zai yi masa magana ba. Mafificin waɗannan masu husumar biyun shi ne wanda zai yi ƙoƙarin gusar da ƙauracewar, kuma ya fara yin sallama, abin nufi da ƙauracewa a nan shi ne na son rai, amma kauracewa saboda haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - kamar ƙauracewa masu saɓo da 'yan bidi'a da mugayen abokai, to, wannan ba a iyakanceshi da wani lokaci, kawai ya na rataya ne da maslaha a ƙauracewar, kuma yana gushewa da gushewarta.

فوائد الحديث

Halaccin ƙauracewa na kwana uku, da ƙasa da hakan, don kula da ɗabi'un mutane, sai akayi afuwa a kan ƙauracewa a cikin kwana uku har wannan abin da ya bijirowar ya tafi.

Falalar sallama, kuma tana gusar da abin da ke cikin zukata, kuma alama ne a kan soyayya.

Kishin musulunci a kan 'yan uwantaka da sabo a tsakanin ma'abotansa.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Al-hajar da Sharaxansa, Ladaban Sallama da Neman izini