إعدادات العرض
Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi
Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە සිංහල ไทย دری Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली тоҷикӣ Oromoo Wolof Soomaali Malagasy Български Українська Azərbaycan ქართული bm Lingala Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi. Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.فوائد الحديث
Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ta inda yake jefa mas'aloli ta hanyar tambaya.
Kyakkyawan ladabin sahabbai tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayin da suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani.
Faɗin wanda aka tamabaya abin da bai sanshi ba; Allah ne mafi sani.
Karewar shari'a ga zamatakewa ta hanyar kare haƙƙoƙi da 'yan uwantaka a tsakaninsu.
Giba abar haramtawa ce sai a wasu halaye dan maslaha; daga hakan akwai: Tunkuɗe zalunci, ta yadda wanda aka zalunta zai ambaci wanda ya zalunceshi ga wanda zai iya karɓa masa haƙƙinsa, sai ya ce: Wane ya zalunceni, ko ya yi min kaza, daga ciki akwai: Shawara a al'amarin aure ko tarayya ko maƙotaka, da makancin hakan.
التصنيفات
Ladaban Magana da kuma shiru