Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta

Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta

Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana nufin kashe abokinsa, to, mai kisan yana cikin wuta saboda kashe abokinsa, sahabbai suka rikita ga wanda aka kashe; Ta yaya zai zama a wuta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa shi ma yana wuta don kwaɗayinsa a kan kashe ɗan uwansa, babu abin da ya hanashi kisan sai gaggawar mai kisan da kuma rigayarsa da yayi.

فوائد الحديث

Cancantar ukuba a kan wanda ya yi ƙudiri a kan saɓo da zuciyarsa, kuma ya aikata sabubbansa.

Gargaɗi mai tsanani daga rigima tsakanin musulmai, da narko na wuta mai tsanani a kansa.

Yaƙi tsakanin musulmai da gaskiya ba ya shiga cikin narkon, misalin yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata.

Mai aikata babban laifi ba ya kafirta saboda aikata saɓon; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambaci masu yakin (da) musulmai.

Idan musulmai suka haɗu ta kowace sila ce a ka yi yaƙi a cikinta, sai ɗayansu ya kashe ɗayan, to, wanda ya yi kisan da wanda a ka kashe suna cikin wuta, ambaton takobi a cikin hadisin ta hanyar misaltawa ne.

التصنيفات

Ayyukan Zukata, Zargin Savo