Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare.

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Ya kasance daga cikin karantarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya ƙin karɓar turare, yana karɓarsa domin yana da sauƙin ɗauka, kuma yana da ƙamshi.

فوائد الحديث

Mustahabbacin karɓar kyautar turare, domin babu wata wahala wurin ɗaukarsa, babu damuwa wurin karɓarshi

Cika da kyakkyawan halin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wurin ƙin karɓar turare da kuma karɓar kyauta daga wanda ya yi masa.

Kwaɗaitarwa a kan amfani da turare.

التصنيفات

Ladaban Ziyara da neman Izini