Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa

Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama. Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa. Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta. Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan. Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.

فوائد الحديث

Girman musulunci a karfafa hakkoki tsakanin musulmai da karfafa 'yan uwantaka da soyayya a tsakaninsu.

التصنيفات

Ladaban Sallama da Neman izini, Ladaban Atishawa da Hamma, Ladaban duba Mara lafiya