Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna

Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna

Daga Sahal Dan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da al'amura biyu idan musulmi ya lazimce su to cewa shi zai shiga aljanna, Na farko: Kiyaye harshe daga maganar da zata fusatar da Allah - Madaukakin sarki -. Na biyu: Kiyaye farji daga afkawa a cikin alfasha. Domin cewa wadannan gabubuwa biyun afkawa cikin sabo da su yana yawaita.

فوائد الحديث

Kiyaye harshe da farji hanya ce ta shiga aljanna.

An kebance harshe da farji; domin cewa su ne mafi girman abinda ke haifar da bala'i ga mutum a duniya da lahira.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta