Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba]

Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba]

Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana aske wani sashi na kai da kuma barin wani sashin. Hanin gamamme ne ga Maza ƙanana da manya, amma ita mace ba ta da damar ta aske kanta.

فوائد الحديث

Kulawar Shari’ar Musulunci da yanayin [mutuntakar] mutum.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Jariri, Munanan Halaye