Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan

Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa aljanna da wuta suna kusa da mutum kamar kusancin igiyar takalmin da yake kasancewa akan bayan kafa, domin kuwa mutum zai iya aikata wani aikin biyayya na yardar Allah - Mai girma da daukaka - da zai shiga aljanna da shi, ko sabon da zai zama sababi na shiga wuta.

فوائد الحديث

Kwadaitarwa a ayyukan alheri koda ya karanta, da tsoratarwa daga sharri koda ya karanta.

Babu makawa ga musulmi a rayuwarsa daga hadawa tsakanin kwadayi da tsoro, da rokon Allah - tsarki ya tabbatar maSa - har abada tabbata akan gaskiya har ya kubuta ba zai rudu da halinsa ba.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta