Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama

Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama

Daga Khaulat Al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labari game da wasu mutane da suke tasarrufi a dukiyoyin musulmai da ɓarna, suna ɗaukarsu ba tare da wani haƙƙi ba, wannan ma'ana ce mai gamewa game da dukiya ta hanyar tara ta da kasuwanci da ita ba tare da halaccinta ba, da ciyar da ita ba ta ingantacciyar hanya ba, cin dukiyoyin marayu da dukiyoyin waƙafi da musanta amanoni da ƙwace ba tare da cancanta ba daga dukiyoyi game gari, to, duk suna shiga cikin wannan. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da labarin cewa sakamakonsu (shi ne) wuta a ranar al-ƙiyama.

فوائد الحديث

Dukiyoyin da ke hannun mutane su ne dukiyar Allah, Ya sanyasu mamaya a kansu don su ciyar da su ta hanyar da aka shara'anta, kuma su nisanci tasarrufi a cikinsu da ɓarna, wannan ya game shugabanni da wasunsu cikin ragowar mutane.

Tsanantawar shari'a a dukiyar al'umma, kuma cewa wanda ya jiɓinci wani abu daga cikinta, to, za a yi masa hisabi a ranar al-ƙiyama a kan samota da kuma ciyar da ita.

Wanda yake tasarrufi tasarrufin da ba na shari'a ba a cikin dukiya ya shiga cikin wannan narkon, duka ɗaya ne dukiyar ta kasance tasa ce ko ta waninsa ce.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Falaloli da Ladabai, Zargin Son Duniya, Zargin Son Duniya