Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba

Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba

Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yanke abin da yake wajaba daga 'yan uwansa na haƙƙoƙi, ko ya cutar da su ya munana musu, to, ya cancanci ba zai shiga aljanna ba.

فوائد الحديث

Yanke zumunci laifi ne daga manyan laifuka.

Sa da zumunci yana kasancewa ne gwargwadon abin da aka yi sabo a kansa, yana banbanta da banbantar wurare da zamaninnika da mutane.

Sa da zumunci yana kasancewa ne da ziyara da sadaka, da kyautatawa garesu, da duba marasa lafiya, da umartarsu da aikin alheri, da hanasu daga abin ƙi, da makamancin hakan.

A duk lokacin da yanke zumuci ya zama da mafi kusanci, to, zai zama ya fi tsananin laifi.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Falaloli da Ladabai, Falalar Sadar da zumunci, Falalar Sadar da zumunci