Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa

Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa

Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira. Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu. Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci. Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.

فوائد الحديث

Rantsuwa mai dulmiyarwa ba ta da kaffara; don tsananin haɗarinta da girmanta, kawai dai akwai [damar] tuba a cikinta.

Taƙaituwa a kan ambaton waɗannan manyan laifukan guda huɗu a hadisin [ya kasance] don girman laifinsu ne, ba don su ne kadai ba.

Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin zunubin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narko da shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasu sun fi wasu muni a haramci.

Kananan zunubai su ne waɗanda ba waɗannan ba.

التصنيفات

Zargin Savo