Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma

Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma

An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"

[Hasan ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a wannan karatun, kuma za a ninka masa lada zuwa ninki goma. Sannan ya yi bayanin hakan da faɗinsa: Ban ce : Alif, Laam, Meem, harafi ba ne, sai dai Alifun harafi ne, Lamun harafi ne, Mimun harafi ne, sai ya kasance harufa uku, lada talatin kenan.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan yawaita karatun Alkur’ani.

Mai karatu a kowanne harafi na kalma da yake rerawa yana da lada da za’a nunka sau goma.

Yalwatuwar rahamar Allah, da kuma karamcinSa, ta yadda ya nunka wa bayinSa lada; falala ce da karamci daga gareShi.

Falalar Alƙur’ani a kan wani zancen da ba shi ba, da yadda ake bauta da karanta shi, saboda shi zancen Allah ne.

التصنيفات

Falalar Kulawa da Al-qur’ani, Falalar al-qur'ani Maigirma