Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka

Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka

Daga Umar ɗan Abu Salama - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance yaro a kulawar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hannuna ya kasance yana yawo a faranti, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka" hakan bai gushe ba shi ne irin cin abincina bayan nan.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Umar Dan Abu Salama - Allah Ya yarda da su - ɗan matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Ummu salamah - Allah Ya yarda da ita - yana ba da labari - (cewa) ya kasance ƙarƙashin renonsa da kulawarsa -, cewa ya kasance a tsakiyar cin abinci yana yawo da hannunsa asasannin ƙwarya (kwanon abin ci) don ya ɗauki abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi ladubba uku daga ladubban cin abinci. Na farkonsu: Faɗin "Da sunan Allah" a farkon ci. Na biyunsu: Cin abinci da dama. Na ukunsu: Cin abinci daga ɓangaren da yake kusa daga gare shi na abincin.

فوائد الحديث

Daga ladubban ci da sha (akwai) ambaton Allah a farkonsa.

Sanar da yara ladubba, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawar mutum.

Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yalwar ƙirjinsa a koyar da yara da ladabtar da su.

Daga ladubban abinci akwai cin abin da ke gaban mutum, sai dai idan ya kasance nau'uka ne da yawa, to, yana da damar da zai ɗauki wanda ya so.

Lazimtar sahabbai da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ladabtar da su da shi, hakan abin fahimta ne daga faɗin Umar: Hakan bai gushe (irin) cin abincina ba bayan nan.

التصنيفات

Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha