Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta

Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsiara da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa wanda ya mutu ba ya hada Allah da kowa to makaomarsa ita ce Aljanna , koda an azabtar da shi akan sashin zunubansa, kuma cewa wanda ya mutu alhali shi yana tarayya da Allah to zai dawwama a wuta.

فوائد الحديث

Falalar Tauhidi, kuma cewa shi sababi ne na tsira daga dawwama a wuta.

Kusancin Aljanna da wuta ga bawa, kuma cewa shi babu wani abu a tsakaninsa da su sai mutuwa.

Gargadi daga shirka, kadan dinta da mai yawanta; domin cewa tsira daga wuta ta hanyar nisantar ta ne.

Izina a ayyuka da karshen su ne.

التصنيفات

Shirka, Sifar Al-janna da Wuta