Ya Rasulallah, Lallai nidai na samu wata kasa a khaibar, kuma ban sami wani kudi ko daya ita ce mafi tsadar abin da na mallaka, mai kake umarta ta da ita?sai ya ce: idan kaso kayi sanya asalinta Hubusi, ko kuma kayi Sadaka da ita

Ya Rasulallah, Lallai nidai na samu wata kasa a khaibar, kuma ban sami wani kudi ko daya ita ce mafi tsadar abin da na mallaka, mai kake umarta ta da ita?sai ya ce: idan kaso kayi sanya asalinta Hubusi, ko kuma kayi Sadaka da ita

Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda da shi- ya ce: "hakika Umar ya sami kasa a khaibar sai ya zo wa Annabi yana neman umarninsa game da ita. sai ya ce: Ya Manzon Allah, Lallai ni na Sami Kasa a Kahibar, kuma ban sami

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Umar Dan Khattab ya sami wata gona a Khaibar, kimarta rabo dari ne kuma ita ce mafi tsadar dukiyarsa, sabida kyawunta da kuma darajarta, kuma Sahabbai sun kasance suna rigen rige wajen yin ayyukan da ladansu zai wanzu sai ya zo Wajen Manzon Allah yana mai kwadayin yin aikin Alkairi irin wanda yake cikin fadin Allah: {Bazaku taba samun ladan Sadaka ba cikakke sai kun ciyar da abinda kuke so} yana neman shawara ta yadda zai yi wannan Sadaka domin Allah, to sai yai masa nuni da Mafi kyawun hanyoyin Sadaka, kuma shi ne yabar Asalin abin kuma yayi wakafinsa, sai Umar yayi hakan, kuma sai ta zamanto Wakafin ta yadda ba zai iya siyar da ita ba ko bayarwa, ko gadarwa, ko wanin hakan daga cikin abubuwan da wanda ya Mallaki abu yake yi, wadanda suke sanya Mulkin abu ya koma hannun wan, ko kuma ya zama Dalilin na komawar, kuma yayi Sadaka da ita ga Talakawa da Miskinai, da kuma Yan uwa, kuma ya fanso wanda yake bawa daga bauta, ko biyan Diyya ga wanda ga wanda ta hau kansa, ko kuma ya taimaki Masu Jahadi a tafarkin Allah da ita, ko kuma ya ciyar da Matafiyi wanda guzurinsa ya yanke zuwa garin da za shi, ko kuma ya ciyar da Bako, domin Girmama Bako yana daga cikin Imani da Allah Madaukaki, kuma kasancewar tana da bukatar wanda zai kula da ita kuma ya rika gyara ta da ban ruwa da noma, kuma da rashin laifi ga wanda yake kula da ita dan yaci wata bukatarsa a ciki gwargwadon bukata, kuma ya ciyar da wani abokinsa ba tare da ya dauki wani abu ba don tara kudi da ita sama da bukatarsa, domin daman ba'a sanya ta ba sai don ciyarwa a hanyoyin Alkairi da kuma kyautatawa, ba don neman kudi ba ko tara Dukiya. Fadakarwa: Wakafi dai shi ne Musulmi yayi Sadaka da wata Dukiya da zata rika bayar da wani amfani ga wasu bangarorin Alkairi, sai ya yi amfani da abinda ta bayar din amma amma Asalin Dukiya tana nan, Misalinsa Mutum yayi Wakafin Gona ga Talakawa, to Yayan Itatuwan da shukar da duk akayi a cikin gonar za'a rabar da shi ne ga Talakawan kuma gonar zata ci gaba da Zama a matsayin Hubusi.

التصنيفات

Waqafi