Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yana da kwatankwacin rabin ladan Mai futa

Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yana da kwatankwacin rabin ladan Mai futa

An rawaito daga Abu Sa'id -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi SAW ya aika uwa Bani Lahyan, sai ya ce:"Lallai daya daga kowane Mutum biyu ya futa, kuma ladan a tsakaninsu" Kuma a cikin wata riwayar: "Lallai daya daga cikin Mutum biyu ya futa" sannan ya ce ga wanda zai zauna: "Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yana da kwatankwacin rabin ladan Mai futa"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Ya zo a cikin Hadisin Abu Sa'id Al-Khudri -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW yai nufin aika Rundunar Yaki zuwa Bani Lihyan, kuma su ne mafi Shaharar Kabilun Huzail, Kuma Malamai sun hadu kan cewa Bani Lihyan sun Kasance a cikin wancan lokaci Kafirai ne, sai ya aika musu da Tawaga da zasu yake su (Sai ya ce) da waccan runduna (Sai Mutum daya daga kowane mutane biyu ya futa) yana nufin daga kowace Kabila rabin Adadinta, (Kuma ladan) ai baki dayan abun da aka samu na Mayaki da wanda bai je ba yana da Alkairi (a tsakanin su) saboda shi ne Ma'anar fadinsa a cikin Hadisin da yake kafinsa "Kuma waye a cikin ya baro Sallama a gidansa da kuma dukiyarsa da Alkairi? to yana da lada kwatankwacin rabin Ladan wanda ya futa" Ma'ana cewa Annabi SAW ya Umarce su da su futar da daya daga cikin su, wani dayan kuma su bar daya ya maye gurbin Mayaki a gidansa, sai ya zamnato yana da rabin ladansa; Saboda rabin ladan na biyun na Mayaki ne

التصنيفات

Falalar Jahadi