Duk wanda aka kirashi da sunan da ba na Mahaifinsa ba -Kuma yana sane cewa ba Mahaifinsa ba ne- To Al-janna ta haramta a gare shi

Duk wanda aka kirashi da sunan da ba na Mahaifinsa ba -Kuma yana sane cewa ba Mahaifinsa ba ne- To Al-janna ta haramta a gare shi

An rawaito daga Sa'ad bn Abi Wakkas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda aka kirashi da sunan da ba na Mahaifinsa ba -Kuma yana sane cewa ba Mahaifinsa ba ne- To Al-janna ta haramta a gare shi"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Kuma wannan Hadisin ya zo don bayanin tsawatarwa daga wani Al-amari da ya Kasance Mutanen Jahiliyya kuma shi ne kiran kai da sunan wanin Mahaifi, saboda Mutum ya Wajaba akan sa ya danganta kansa da Ahalinsa Babansa kakansa da kuma kakan Babansa, da kuma abunda yayi Kama da hakan kuma bai halatta gare shi ba, ya danganta kansa ba zuwa wanin Babansa kuma shi yana Sane cewa ba Babansa Misali idan ya kasance Babansa yana Kabila Kaza kuma ya ga cewa wannan Kabila akwai Tawaya kan wata Kabilar sai ya danganta zuwa wata Kabila ta biyu sama da Daraja, Saboda ya gusarwa kansa Wani aibun Kabilarsa, Saboda wannan ana jan kunnensa da Haramta Masa Al-janna

التصنيفات

La'ani