Duk wanda ya yi Azumi daya Saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo tsakaninsa da Wuta kamar nisan Sama da Kasa

Duk wanda ya yi Azumi daya Saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo tsakaninsa da Wuta kamar nisan Sama da Kasa

An karbo daga Abu Umama -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya yi Azumi daya Saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo tsakaninsa da Wuta kamar nisan Sama da Kasa"

[Hasan ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Cikin wannan Hadisin akwai Bayanin Falalar Azumin wata Rana daya Sabida Allah, yadda Allah zai tserar da shi daga Wuta kuma ya nisanta shi ga barinta Kamar nisan sama da Kasa.

التصنيفات

Falalar Azumi