Ni nasan in kina farin ciki dani, kuma haka idan kina fushi da ni

Ni nasan in kina farin ciki dani, kuma haka idan kina fushi da ni

An karvo -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Ni nasan in kina farin ciki dani, kuma haka idan kina fushi da ni" sai ta ce: sai na ce: ta yaya kake gane hakan ? sai ya ce: "Idan kina farin ciki sai kice a'a na rantse da Muhammad kuma idan kina fushi da ni sai ki ce na Rantse da ubangijin Ibrahim" sai ta ce: na ce: Ey wallahi haka ne ya Manzon Allah, bana qauracewa sai sunanka

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya ce da ni: "Lallai ni ne mafi sanin lokacon da bakya fushi da ni, da kuma lokacin da kike fushin da ni, sai ta ce da shi: ta yaya ka sani hakan? sa i Manzon Allah SAW ya ce: "idan kina fushi da ni awani kina cewa: Na rantse da Ubangijin Muhammadu, sai ki kirawo sunana a cikin rantsuwarki, kuma idan kina fushi da ni akan wani abu na duniya da yake da alakar zamantakewar Aure, sai ki ce a cikin rantsuwarki: na rantse da Ubangijin Ibrahim, sai ki kaucewa faxar suna na zuwa sunan Ibrahim sai ta ce: E haka ne Wallahi ya Manzon Allah, ba zan bari ba sai faxar sunanka akan Harshena tsawon fushi na, sai dai Soyayyarka tana nan daram cikin Zuciyata

التصنيفات

Matansa SAW da halin gidan Annabta