"Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"

"Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"

An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"

[Ingantacce ne ta wani bangaren] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Hadisin yana nuna cewa duk wanda ya tuna Allah to Allah zai kasance kusa da shi, kuma zai kasance tare da shi a kowane Al-amuransa, Saboda zai datar da shi kuma ya shirye shi kuma ya taimake shi ya amsa Addu'arsa, kuma Ma'anar wannan Hadisin ta zo a cikin wani hadisin a cikin sahihul Bukhari Manzon Allah ya ce: "Ni ina inda Bawa na ya Zace ni kuma ni ina tare da shi a duk lokacin da ya anbaceni a , idan ya anbaceni cikin Ransa to zan anbace shi cikin raina, in kuma ya anbace ni cikin Mutane zan anbace shi cikin Mutanen da suka fi nasa Al-kairi

التصنيفات

Falalar Zikiri