إعدادات العرض
"Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina"
"Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina"
An rawaito daga Abu Musa Al-Ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce Annabi SAW ya ce: "Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina sai su hada abunda yake wurin su a cikin Zani daya, sannan sai su raba shi tsakaninsu acikin kwarya daya, daidai da dai dai, Saboda haka ni daga cikin su nake suma kuma nawa ne"
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî தமிழ்الشرح
Lallai Ash'ariyawa, wadanda su ne mutanen Abu Musa, yardar Allah ta tabbata a gare shi, idan abincinsu ya ragu ko kuma suna cikin mamayar jihadi saboda Allah, sai su tattara abincinsu su raba daidai a tsakaninsu, don haka sun cancanci ba wa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wani kaso na girmamawa da soyayya, kuma shi ma yana cikinsu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, gwargwadon hanyar su a wannan. kuma wajibine na biyayya.