"Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi"

"Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi"

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- daga Annabi: "Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi, saboda dayanku idan yayi Sallah yana gyangyadi bai san watakila yaje yana neman Istigfari sai ya zagi kansa (Maimakon haka)"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abunda Hadisin yake nunawa kin wahalar da kai a Ibada sai mai Sallah yaji da Alamar rinjayar Bacci kuma shi yana Sallah sai ya yanke sallarsa ko ya cika ta sannan ya kwanta ya hutar da kansa, har don kada wani abu ya same shi na rashin dadi Addu'a halin gajiyarsa

التصنيفات

Falalar musulunci da kyawawan koyarwarsa, Tsayuwar Dare