Mun kasance Muna yiwa Annabi SAW Mubaya'a kan ji dabiyayya, yana cewa da mu cikin abunda zaku iya

Mun kasance Muna yiwa Annabi SAW Mubaya'a kan ji dabiyayya, yana cewa da mu cikin abunda zaku iya

Daga Ibn Umar -Allah ya yarda da su- "Mun kasance Muna yiwa Annabi SAW Mubaya'a kan ji dabiyayya, yana cewa da mu cikin abunda zaku iya"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Ibn Umar -Allah ya yarda da su- yana bada labari cewa su idan suka yiwa annabi Mubaya'a yana umartar su da ji da kuma biyayya gwargwadon iko, kuma cewa shi idan aka dorawa Musulmi da abunda ba zai yi wu ba, to babu biyayya akan ta, (Allah ba ya dorawa rai sai abunda zai iya).

التصنيفات

Haqqin Shugaba kan Talakawa