Lallai ruwa baya yin Najasa

Lallai ruwa baya yin Najasa

An karvo daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: wasu daga cikin Matan Annabi SAW sunyi Wanka a cikin Daro, sai Manzon Allah ya zo zai yi Al-wala daga ciki ko zai yi wanka, sai ta ce da shi: Ya manzon Allah nifa na kasance ina da janaba? sai Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai ruwa baya yin Najasa"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Xaya daga cikin Matan Manzon Allah SAW tayi Wankan Janaba, sai Manzon Allah SAW yazo zaiyi Al-wala ko wanka; sai yaso yayi amfani da ruwan da ya ragu na ruwan Wankan Matarsa -Allah ya yarda da ita- sai ta gaya masa cewa ita ta kasance tana da Janaba, sai ya nusar da ita cewa hakan ba zaiyi tasiri a ruwan ba, kasancewar sa mai tsarki kuma abun tsarkakewa

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Ruwa