Waxanda suke zage zage abunda suka faxa to wanda ya fara daga cikinsu yana kansa har sai wanda aka zaga ya rama

Waxanda suke zage zage abunda suka faxa to wanda ya fara daga cikinsu yana kansa har sai wanda aka zaga ya rama

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi Amincin Allah a gare shi ya ce: "Waxanda suke zage zage abunda suka faxa to wanda ya fara daga cikinsu yana kansa har sai wanda aka zaga ya rama"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Duk abin da masu zage zagen sukai Musaya, zunubin hakan yana kan wanda ya fara su; Saboda shi mai zalunci ne ta hanyar aikinsa, alhali kuwa dayan ba lallai bane ya aikata shi; Saboda yana da izini ya mayar da martani ga wadanda suka zalunce shi, idan wanda aka zalunta ya afkawa Azzalumi ta hanyar wuce iyaka da aka ba shi, to zunubin wanda aka zalunta ya zama ya fi na wanda ya fara shi

التصنيفات

Munanan Halaye, Ladaban Magana da kuma shiru