Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa

Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa

Daga Ubaidullahi Ibnu Adi Ibnul Khiyar ya ce: Wasu mutane biyu sun bani labarin cewa sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana alhali shi yana raba sadaka (zakka), sai suka tambaye shi zakkar, sai ya ɗaga idanuwansa garemu ya kuma yi ƙasa da su, sai ya ganmu ƙarfafa ne, sai ya ce: «Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa».

[Ingantacce ne] [رواه أبو داود والنسائي]

الشرح

Wasu mutane biyu sun zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana, alhali shi yana raba sadaka (zakka), kuma suka nemi ya basu daga cikin zakkar, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sake kallonsu, dan ya gane halinsu, kuma shin ya halatta a basu sadakar ko a'a? Sai ya gansu mazaje ne biyu ƙarfafa, sai ya ce: Idan kuna so zan baku daga cikin zakkar, babu rabo a cikinta ga wanda yake da dukiyar da zata ishe shi, ko ga wanda yake da ikon yin aiki ko juya dukiya, ko da ba shi da dukiyar da za'a ɗauke shi (a matsayin) mawadaci da ita.

فوائد الحديث

Haramcin roƙo ga mutum mawadaci ko ƙaƙƙarfan da zai iya neman na-kansa.

Asali ga wanda ba’a san yana da dukiyaba to talaka ne da kuma cancantar karɓar sadaka.

Mujarradin ƙarfi ba ya hukunta rashin cancantar karɓar sadaka, kai babu makawa da a haɗa da iko akan iya nema.

Mai iko akan neman abin da zai ishe shi ba ya halatta ya karɓi sadaka ta wajibi (wato Zakkah); dan wadatuwarsa da neman na kansa, kamar wadatuwar mawadaci ne da dukiya.

Tarbiyyar Annabi mai girma ga mutum musulmi akan kamewa, da kuma bayarwa banda karɓa da roƙo da kuma kasala.

التصنيفات

Waxanda za'a bawa Zakka