إعدادات العرض
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, amma ba Najjashin da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sallah ba.
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahiliالشرح
Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin rasuwarsa ya yi rubutu zuwa ga waɗanda ke kewaye da shi daga sarakunan al'ummu, yana kiransu zuwa ga Musulunci; sai ya rubuta zuwa ga Kisra, shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Farisawa, haka zuwa ga Ƙaisara shi kuma laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Rum, haka zuwa ga Najjashi shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Habasha. Kuma ya rubuta zuwa ga kowane sarki mai tsaurin kai wanda ya yi wa mutane tumbe, ya rinjaye su, kuma Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bayyana cewa Najjashin da aka rubuta masa ba Najjashin da ya musulunta ba ne kuma ya rasu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa sallah.فوائد الحديث
Halaccin kiran waɗanda ba musulmai ba zuwa Musulunci, wanda ya haɗa manyan sarakunansu da kuma ƙananan sarakuna.
Halaccin yin aiki da littafi da kuma wasiƙu.
التصنيفات
Wasiqunsa da aikensa SAW