إعدادات العرض
1- "Lallai cewa Manzon Allah ya hana Al-Munabaza: Kuma yana nufin Mutum ya jefa Rigarsa zuwa wani Mutum kafin ya juyashi, ko ya dubashi, kuma ya hana Al-Mulamasa: kuma yana nufin Mutum ya taba Tufa ba zai kalle ta ba"
2- "Lallai Manzon Allah ya hana saida "yayan Itatuwa har sai sun bura, aka ce Maye Bura din yace har sai ya fara yin ja, ya ce baka ganin idan Allah ya hana 'yayan Itattun suyi, to da me mutum zai rama kudin Dan Uwansa?
3- Cewa - Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana sai da yayan itace har sai sun bura ya hana mai saye da kuma mai sayarwa
4- Annabi ya hana Dan Gari ya siyarwa da Dan Kauye, (kayansa a Kasuwa), kuma kada kuyi keta, kuma kada wani daga cikinku yayi ciniki akan cinikin Dan Uwansa, kuma kada ya nemi Aure kan neman Auren Dan Uwansa
5- "lallai Annabi ya Hana siyar da Walittaka ko kyautarta"
6- Ka ku tari hanya, kuma kada dayanku yayi cikin akan cinikin Dan uwansa, kuma kada kuyi keta, kuma kada Mutumin birni ya siyarwa da Mutumin kauye kayansa, kuma kada ku daure hantsar rakuma ko dabbobi