Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar rigima a kofar gidansa

Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar rigima a kofar gidansa

Daga Ummusalama -Allah ya yarda da ita- cewa Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agare shi ya ji hayaniyar husuma a kofar gidnsa sai ya fito wajen su, yace: "ku saurara lallai Ni mutum ne, tana yiwuwa masu husuma su zo min,kuma waninku ya fi wani iya magana, sai na yi tsammani shi ne mai gaskiya sai in bashi gaskiya to duk wanda na bashi gaskiya, alhali ba shi ne mai gaskiya ba, to ya sani yankin wuta ne, ko ya dauka ko ya bari,

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ji hayaniyar masu rigima,a kofar gidansa,sai ya fito don ya yi musu hukunci a tsakanin su sai yace: Lallai Ni mutum ne kamar ku, ban san gaibu ba, bana bada labarin boyayyayun al'amura, ban san waye mai gaskiya ko makaryaci a cikinku ba, masu rigima sukan zo dan na yi hikunci a tsakaninsu,kuma hukunci na yana kasancewa ne akan abin da na ji daga kowane bangare, da rantsuwoyinsu, kuma yana iya kasancewa wani yafi wani iya magana sai na zaci shi ne mai gaskiya sai na bashi gaskiya,tare da cewa abokin fadan shi ne mai gaskiya, ku sani ina hukunci da abubuwan da suke bayyane ne ba da wanda suke boye ba, ba zai halarta haram ba, don haka duk wanda na bawa gaskiya alhali ya san shi ne marar gaskiya, to yasan cewa wani yanki na wuta ne na yanko masa, in ya so sai ya dauka ko ya bari, sakamakon hakan na komawa akansa, Allah na jiran azzalumai a madakata

التصنيفات

Da'awa da kuma Dalilai