إعدادات العرض
Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi bai taba sabo da wani abu na nafila ba, irin yadda ya saba da Raka'oi biyu na alfijir
Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi bai taba sabo da wani abu na nafila ba, irin yadda ya saba da Raka'oi biyu na alfijir
Daga Aisha 'yar Abubakar Assiddik -Allah ya yarda da ita- tace: "Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi bai taba sabo da wani abu na nafila ba, irin yadda ya saba da Raka'oi biyu na alfiji". A wata ruwayar kuma: "Raka'o'i biyu na bayan Alfijir sun fi duniya da abin da ke cikinta alheri".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdîالشرح
Wannan hadisai biyu suna bayanin muhimmancin raka'o'i biyu na bayan alfijir, Aisha Allah ya yarda da ita ta ambaci ya tabbatar da muhimmancinsu da girman darajarsu ta hanyar aikata su da yake yi, baya fasa yin su, kuma ya bayyan cewa sune mafi alherin dauniya da abin da ke cikinsu.