Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne

Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa cin abinci sau biyu ba a rana ɗaya sai ɗayan ya zama dabino ne.

فوائد الحديث

Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da iyalan gidansa, sauda yawa a rana ɗaya ma basu samun wani abin da zasu ci sai abinci ɗaya.

Dabino ya kasance shine mafi sauƙi a wurinsu akan waninsa.

Falalar gudun duniya da wadatuwa da kaɗan a rayuwa, kuma kasancewarsa yana daga ɗabi'un Annabawa, da kuma tarihin shugaban Manzanni.

Cin abinci sau biyu a rana ɗaya yana daga cikin al'amuran da aka halatta, kuma hakan yana daga cikin sanannun al'adun larabawa, domin sun kasance a rana ɗaya suna ci ne sau biyu, abincin rana da abincin dare.

التصنيفات

Zuhudu da tsantseni, Shiryarawar Annabi