إعدادات العرض
Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama
Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce: Ya Manzon Allah ka yi wa mushrikai mummunar addu'a ya ce: "Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული Kurdî বাংলা ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahili ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતીالشرح
An nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mushrikai mummunar addu'a, sai ya ce: Lallai cewa ni ba'a aikoni daga Allah in zama mai yawan tsinuwa ba ina yi wa mutane mummunar addu'a da nisantarwa da kuma korewa daga rahamar Allah sai in yanke su daga alheri, lallai ni ba'a aikoni dan haka ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama sababin alheri da kuma rahama ga mutane baki ɗaya, da kuma muminai a keɓance.فوائد الحديث
Cikar ɗabi'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Muhimmancin tsaftace harshe daga zagi da tsinuwa dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
A cikinsa akwai hani daga tsinuwa.
Kwaɗaitarwa akan jin ƙan mutane.
التصنيفات
Shiryarawar Annabi