Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi.

Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi.

Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi ya ce: "Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana bamu labari acikin wannan Hadisi cewa Mumini wani lokaci wani abu na masibu yakan same shi akansa ko Dukiyarsa ko waninsa, kuma cewa Allah zai bashi lada akan kowace Musiba ce ta Sameshi, Sannan ya bayyana cewa Musibu koyaushe suka zamo Manya kuma hadarin su ya girmama to ladansu yakan girmama a wajen Allah Sannan Annabi yayi bayanin cewa cewa afkuwar Musibu yana daga cikin Alamomin Son Allah ga Mumini, Kuma Hukunin Allah da Kaddararsa babu Makawa sai sun afku, sai dai kuma wanda yayi Hakuri kuma ya yarda da Kaddarar , to Allah zai saka masa kan hakan da Yardarsa kuma babu ladan da yafi wannan, kuma duk wanda ya yayi fushi kuma yaki yarda da Kaddarar Allah to Allah zai fushi da shi , kuma babu ukubar da tafi wannan.

التصنيفات

Imani da Hukuncin Allah da Qaddara