Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an ba shi daga cikin ayoyi waɗanda mutane za su yi imani da shi

Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an ba shi daga cikin ayoyi waɗanda mutane za su yi imani da shi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an ba shi daga cikin ayoyi waɗanda mutane za su yi imani da shi, ni kuma abin da aka bani shi ne wahayi da Allah Ya yi mini wahayi ina fatan na fisu mabiya ranar alƙiyama».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa Annabawa dukkaninsu Allah Ya ƙarfafesu kuma Ya basu ayoyi da mu'ujizoji waɗanda suka saɓawa al'adu waɗanda ake kafa hujja da su akan Annabtarsu, kuma suna hukunta imanin wanda ya gansu ya gasgatasu, kuma cewa shi abin rinjaye ne a kansa a cikin kalubalantar inda ba zai iya tunkuɗesu ba akan kansa, sai dai zai iya musantasu kuma ya yi tsaurin kai. Kawai shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayarsa da mu'ujizarsa ita ce Alƙur'anin da Allah Ya yi masa wahayinsa; saboda abin da ya ƙunsa na gajiyarwa mabayyaniya tabbatacciya saboda yawan fa'idarsa da kuma gamewar amfaninsa, dan abin da ya ƙunsa akan Da’awah da hujja da kuma bada labarin abin da zai kasance, sai amfaninsa ya game wanda ya halarta da wanda baya nan da wanda aka samu da wanda za'a samu, sannan ya ce: Ina fatan in zama na fisu yawan mabiya a ranar alƙiyama.

فوائد الحديث

Tabbatar da ayoyi ga Annabwa, wannan yana daga rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma falalarSa akan al’ummu.

Bayanin girman mu'ujizar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Bayanin girman matsayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma fifikonsa akan ragowar Annabawa.

Ibnu Hajar ya faɗa a cikin faɗinsa: "Kaɗai abin da aka bani ya kasance wani wahayi ne wanda Allah Ya yi mini shi": Bawai ana nufin taƙaita mu'ujizojinsa a cikinsa ba, kuma bawai cewa ba'a bask shi mu'ujizojin da aka bawa waɗanda suka gabace shi ba, kai abin nufi cewa hakan mu'ujiza ce babba wacce ya keɓanta da ita banda waninsa.

Nawawi ya ce; "(Ina fatan in zama na fisu yawan mabiya) alama ce daga cikin almomin Annabta, domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari da wannan a zamanin ƙarancin musulmai, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Yayi masa baiwa Yayi buɗi ga musulmai, kuma Yayi albarka a cikinsu har sai da al'amari ya kai makura al'amari ya yalwatu a cikin musulmai har zuwa wannan kololuwar da aka sani, godiya ta tabbata ga Allah.

التصنيفات

Annabinmu Muhammad SAW