Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai

Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda yake cikin masallaci ya fara yin sallar nafila bayan an yi iƙamar sallar farilla.

فوائد الحديث

Hani daga yin sallar nafila idan an yi iƙamar sallar farilla alhali shi yana cikin masallaci.

Hani akan fara nafila bayan an yi iƙamar sallah, daidai ne ta kasance ratiba ce kamar sunnar Asuba da Azahar ko waninta.

Idan an yi iƙamar sallah alhali shi yana yin nafila; idan mafi ƙaranci daga raka'a ya rage to ya cikata a sauƙaƙe, inba haka ba to sai ya yanketa har ya riski falalar kabbarar harama.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta